Shafin Facebook na cikin tsaka mai wuya

Wannan ya kasance makon da kamfanonin fasaha da yawa suka nuna damuwarsu kan yadda za su fuskanci al’amuran bambancin launin fata da na siyasa.

A wannan makon, wasu daga cikin ma’aikatan kamfanin Facebook sun bijire wa manufofin kamfanin.

Kamfanin Twitter kuwa ya auka wani yakin cacar baki da Shugaba Trump bayan da kamfanin ya gargade shi cewa wasu sakonni da ya wallafa na iya tayar da hankalin jama’a.

A halin yanzu, Mark Zuckerberg da alama zai kauce wa irin yaƙin cacar bakin, bayan da ya bayyana cewa Facebook ba zai bi irin hanyar da Twitter ya bi ba.

Amma sai ga shi yana fuskantar tawaye daga bangaren da bai zata ba.

Cigaban Labari

Check Also

shafin google zai dakatar da tallan siyasa

Shafin Google zai dakatar da tallace-tallacen Siyasa

Kamfanin Google ya sanar da kudirinsa na dakatar da duk wasu tallace-tallace da suka shafi …

error: Alert: Is not allowed !!!