Shugaba Muhammadu Buhari ya yaba da yadda aka gudanar da zaben Jamhuriyar Nijar cikin kwanciyar hankali…

Shugaba Muhammadu Buhari ya yaba da yadda aka gudanar da zaben Jamhuriyar Nijar cikin kwanciyar hankali, yayin ganawa da shugaban tawagar kungiyar ECOWAS wajen sanya ido a zaben Arch Namadi Sambo. 

Buhari yace sun damu kwarai da zaman lafiyar Jamhuriyar Nijar, saboda haka ya bayyana jin dadin sa da yadda aka kammala zaben ba tare da samun tashin hankali ba, kamar yadda masu sanya ido suka tabbatar.

Shugaban ya kuma yabawa Namadi Sambo da tawagar sa ta ECOWAS kan rawar da suka taka wajen ganin kawo masa kyakyawar labarin abubuwan da suka faru.

Yayin jawabin sa, Namadi Sambo yace sun sanya ido a mazabu kusan 400 a fadin kasar, kuma sun gamsu da yadda al’amura suka gudana da yadda aka baiwa kowanne dan kasa damar sauke nauyin sa.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo yace an samu gagarumun cigaba a zagaye na biyu na zaben, sabanin wanda aka gani ranar 27 ga watan Disambar bara.

Check Also

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo mai shekara …

error: Alert: Is not allowed !!!