Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano Farfesa Garba Ibrahim Sheka (KANSIEC) ta ce…

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano Farfesa Garba Ibrahim Sheka (KANSIEC) ta ce yanayin matsin tattalin arzikin da kasa ta shiga ne ya sa ta gaza biyan ma’aikatanta na wucin gadi da suka yi aikin zaben Kananan Hukumomi a jihar hakkokinsu.

Hakan na zuwa ne bayan shafe kusan makonni bakwai da kammala zaben, duk kuwa da cewa an ware wa hukumar Naira biliyan biyu da miliyan 300 domin shirya zaben.

Farfesa Sheka ya ce KANSIEC ta damu matuka kan tsaikon da aka samu kan biyan ma’aikatan hakkokin nasu, inda ya ce sun fara biyan wasu daga cikinsu kuma za su kammala na ragowar nan ba da jimawa ba.

Check Also

IMG Spraker Falgore

Capacity building ; a morale booster for effective service delivery.. Speaker Falgore.

From the Legislative House, Kano State House of Assembly. Capacity building ; a morale booster …