Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kwantar da hankali bayan zanga-zangar EndSARS.

Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a sanarwar da mai bashi shawara  Femi Adesina ya aike wa manema labarai ranar Laraba.

“Fadar shugaban kasa tana rokon jama’a da su kwantar da hankali, a yayin da shirin kawo sauyi kan harkokin ‘yan sanda ke ci gaba da wakana a matakin gwamnatin tarayya da na jihohi”, in ji sanarwar.

Ya yaba wa jihohin da suka kaddamar da kwamitocin yin garanbawul ga rundunar ‘yan sanda, yana mai cewa hakan ya nuna cewa a shirye suke su aiwatar da sauye-sauyen.”

A lissafinmu na karshe, jihohin da ba su gaza 13 ba sun kaddamar da kwamitocin shari’a domin samar da mafita da kuma yin adalci ga mutanen da ‘yan sanda suka musgunawa kamar yadda Majalisar Tattalin Arziki ta nemi su yi,” a cewar Shugaba Buhari.

Kawo yanzu jihohin da suka kafa kwamitocin sun ƙunshi Lagos, Kaduna, Delta, Ekiti, Ogun, Anambra, Enugu, Imo, Plateau, Edo, Nasarawa, Ondo da kuma Akwa Ibom.Shugaba Buhari ya kara da cewa gwamnatinsa ta dade tana fafutukar ganin an kawo sauyi kan ayyukan ‘yan sandan Najeriya, ciki har da matakan da suka dauka na kafa kwamitin shari’a da zai tattabar da adalci kan mutanen da ‘yan sanda suka ci zarafi a jihohi da kuma sanya hannu kan kudurin dokar samar da gidauniyar ‘yan sanda.

Kazalika a shekarar 2018, Shugaba Buhari ya amince a kara albashin ‘yan sanda inda aka kara kasafin kudinsu na shekara-shekara daga naira biliyan 288 a 2018 zuwa naira biliyan 417 a kasafin kudin 2021; karin kashi 45 cikin dari, in ji sanarwar.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a yayin da ake zargi sojojn Najeriya sun bude wuta kan dubban masu zanga-zangar EndSARS a birnin Lagos ranar Talata lamarin da rahotanni suka ce ya yi sanadin mutuwa akalla 12 da jikkatar mutane da dama.

Kazalika kiran nasa na zuwa ne a daidai lokacin da jihohin da dama suka sanya dokar hana fita da zummar takaita bazuwar zanga-zangar wadda aka soma mako uku da suka gabata.

 

Check Also

IMG Spraker Falgore

Capacity building ; a morale booster for effective service delivery.. Speaker Falgore.

From the Legislative House, Kano State House of Assembly. Capacity building ; a morale booster …