Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Daniel Levy yana son ya jira zuwa karshen kakar wasan bana…

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Daniel Levy yana son ya jira zuwa karshen kakar wasan bana kafin yanke shawara kan matsayin mai horas da kungiyar Jose Mourinho.

Dan wasan Argentina Sergio Aguero, mai shekara 32, ya ce ba shi da tabbacin ci gaba da zama a Manchester City bayan karshen kakar wasan da muke ciki.

Kocin Chelsea Thomas Tuchel yana son dan wasan Amurka Christian Pulisic, mai shekara 22, ya ci gaba da zama a Stamford Bridge, amma ya kara da cewa ba a yanke wata shawara ba game da kakar wasan da muke ciki

Golan Chelsea dan kasar Sifaniya Kepa Arrizabalaga, mai shekara 26, ya yi ikirarin cewa bai taba cewa zai bar kungiyar ba kuma ba ya shakkar fafatawa domin komawa matsayinsa.

Borussia Dortmund za ta gwammace ta sayar da dan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 20, sannan ta ci gaba da rike dan wasan Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 20, a bazarar nan.

Check Also

Gwamantin Tarayya ta ce ba za ta tattauna da ’yan bindiga da ke addabar sassan kasar nan. Yayin jawabi ga Taron Tattaunawa kan Taron Kasa a Fadar Shugaban Kasa, Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, Janar Babagana Monguno (mai ritayi) ya yi fatali ta batun sulhu da ’yan bindiga. Fitaccen malamin Islama, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, wanda kuma tsohon hafsan soja ne na daga cikin masu ba da shawarar tattaunawar sulhu da ’yan bindigar domin a samu zama lafiya. Amma da yake bayani a Fadar Shugaban Kasa a jiya Laraba, Monguno ya ce yin sulhu zai sa ’yan bindigar su yi zaton cewa gwamanti ta gaza. Ya ce, “Gwamnati na kokarin shawo kan matsalar tsaro, kuma sun sha bayyana cewa akwai matakai biyu na magance ta –lallami, tattaunawa, da sauransu. Duk da cewa gwamnati ba ta adawa da tattaunawa da su, amma tsakanin da Allah dole gwamnati ta yi amfani da karfi a kan wadannan mutane saboda ba su da amana, tunda za’a yi magana da su amma su je su wani na daban kuma su ci gaba da cutar da al’umma

Gwamnatin Tarayya tace babu shulhu tsakanin ta da ’yan bindiga da ke addabar sassan kasar nan

Gwamantin Tarayya ta ce ba za ta tattauna da ’yan bindiga da ke addabar sassan …

error: Alert: Is not allowed !!!