Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya bukaci a sauya tsarin hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya bukaci a sauya tsarin hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA don rage yawan masu sayar da miyagun kwayoyi.

Shugaban majalisar yayi wannan batu ne a lokacin da shugaban hukumar NDLEA, Buba Marwa ya kai masa ziyara majalisar a ranar Alhamis.

A wata takarda wacce hadimin shugaban majalisar dattawa na musamman, Ezrel Tabiowo ya fitar ya bayyana shugaban na cewa masu sayar da miyagun kwayoyi sun baje kolinsu a kasar nan.

Lawan ya bukaci a sauya tsarin NDLEA, a kara wa hukumar karfi don kawo karshen siye da siyar da miyagun kwayoyi a kasarnan.

A cewarsa, majalisar dattawa zata bayar da gudun mawa kwarai wurin kawo gyara ga hukumar NDLEA.

Lawan ya kara nuna muhimmancin hada kai da duk jami’an tsaron gwamnati don kawo karshen rashin tsaro, karancin ilimi, rashin ayyukan yi da fatara.

 

 

Check Also

IMG Spraker Falgore

Capacity building ; a morale booster for effective service delivery.. Speaker Falgore.

From the Legislative House, Kano State House of Assembly. Capacity building ; a morale booster …