Sojoji sun Ragargaji ‘Yan bindiga a Jahar Katsina

Rundunar sojin Najeriya sun yi gagarumin nasara a kan yan bindiga a Katsina – Sojoji sun ragargaji ‘yan bindigan, sun kawar da wasu da dama sannan sun kwato makamai. Hakan na daga cikin kokarin da suke na kawar da ta’addanci da sauran muggan laifuka a arewa maso yamma Jami’an atisayen ACCORD sun kawar da wasu ƴan bindiga daɗi,sun kama wasu da ake zargi da kuma sun kwace makamai a Jihar Katsina.

Acigaba da ake na atisayen kawar da ta’addanci da sauran muggan laifuka a arewa maso yamma na ƙasar Najeriya,jami’an atisayen ACCORD sun sami gagurumar nasara.

Jami’an Atisayen ACCORD a ranar 15 ga watan Nuwamba 2020 lokacin wani sumamen dare a ƙauyen Ƴar Tasha sun yi kiciɓus da ƴan bindiga daɗi inda akayi musayar wuta. Lokacin musayar wutar,an sheƙe uku daga cikin ƴan bindiga daɗi,inda wasu daga cikinsu suka tsere da munanan raunuka sanadiyyar harbin bindiga.

An samu nasar ƙwace bindigu ƙirar AK 47 guda 3 lokacin da akayi musayar wuta daga hannun miyagun. A wani cigaban kuma,bayan samun bayanan sirri akan motsin ƴan bindiga daɗin,sojoji sun gudanar da sumamen farmaki tsakanin ƙauyukan Natsinta da Dawanna a ƙaramar hukumar Jibia tsakanin titin Katsina zuwa Jibia.

A wannan atisayen,sojoji sunyi nasarar daƙume ƴan bindiga daɗi guda 10,lokacin da suke ƙoƙarin yin hijira tare da dabbobin da suka kwace. Lokacin da ake tuhumar su,bayan da gyaɗa taji matsa,bakwai (7) daga cikinsu sunce sunyo hijira ne daga ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara zuwa jamhuriyyar Nijar.

An kama waɗanda ake zargin da shanu 88 da tumaki wanda ba’a gano adadinsu ba.Yanzu haka waɗanda ake zargin suna hannun hukuma ana cigaba da gudanar da bincike. Hakazalika,sojojin da aka kai Unguwan Doka a ranar 15 ga watan Nuwamba 2020,sun ceto wani mutum da aka sace mai suna Adamu Yahaya.

Check Also

Tattaunawa da Matashi Mai Dalilin Aure dan Shekaru 23

AR_ Gabatar mana da kanka da kuma aikace aikace da kake yi. Auwal_ sunana Auwal …

error: Alert: Is not allowed !!!