Sojojin kasarnan da ke yaƙi da Boko Haram sun mamaye wata gona da suka ce ta Abubakar Shekau ce a dajin Sambisa.

Sojojin kasarnan da ke yaƙi da Boko Haram a yankin arewa maso gabas sun mamaye wata gona da suka ce ta Abubakar Shekau ce a dajin Sambisa.

Wani bidiyo da jaridar PRNigeria ta ce ta samu ya nuna yadda sojojin suka abka wa gonar da wasu kamar fararen hula suna kwasar amfanin gona.

A cikin bidiyon an ji sojojin na harbin bindiga suna yi wa shugaban Boko Haram Abubakar Shekau shaguɓe cewa ya fito daga inda yake ɓuya.

Inda suke cewa Shekau Ba ka ce ka shirya za ka yi shahada ba, ka fito mu barar da kai.

Jaridar PRNigeria ta ce bayan sojojin sun murƙushe wani hari a Dikwa sun kuma kama wasu masu taimakawa ƙungiyar ISWAP da bayanai.

Check Also

IMG Spraker Falgore

Capacity building ; a morale booster for effective service delivery.. Speaker Falgore.

From the Legislative House, Kano State House of Assembly. Capacity building ; a morale booster …