Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu, ya bayyana wa babbar kotun tarayya da ke Abuja cewa doka ta ba shi damar ci gaba da kasancewa a ofis har zuwa 2023 ko 2024.

Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu, ya bayyana wa babbar kotun tarayya da ke Abuja cewa doka ta ba shi damar ci gaba da kasancewa a ofis har zuwa 2023 ko 2024.

Ya bayyana hakan ne a cikin takardun kotu da ya gabatar don kalubalantar karar da ke kalubalantar karin wa’adin watanni uku da Shugaba Muhammadu Buhari ya ba shi a watan Fabrairu.

Jaridar Premium Times ta samu takardar kin amincewar ta farko tare da rakiyar takaddun da Sufeton ya gabatar, ta hannun lauyan sa, Alex Izinyon, wani Babban Lauyan a kasar nan.

Mista Adamu ya cika shekaru 35 a kan aiki a ranar 1 ga Fabrairu, amma ya samu karin wa’adin watanni uku daga Shugaba Muhammadu Buhari a ranar 3 ga Fabrairu.

An ruwaito cewa wani lauya mazaunin Abuja, Maxwell Opara, ya shigar da kara a ranar 3 ga watan Fabrairun don kalubalantar tsawaita wa’adin.

Opara ya ta cikin takardar shigar da kara ya bayyana cewa sashi na 215 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da kuma sashi na 7 na Dokar ‘Yan Sandan Najeriya, 2020, Mista Adamu ba zai iya ci gaba da aikinsa ba kasancewar ya kamata ya yi ritaya a watan.

Amma Mista Adamu ya musanta hakan ta bakin lauyansa, cewa lokacin nasa bai kare ba a ranar 1 ga Fabrairu. Sufeton ya cewa sabuwar dokar ‘yan sandan Najeriya ta ba shi wa’adin shekaru hudu wanda ba zai kare ba har 2023 ko 2024.

Check Also

IMG Spraker Falgore

Capacity building ; a morale booster for effective service delivery.. Speaker Falgore.

From the Legislative House, Kano State House of Assembly. Capacity building ; a morale booster …