Takaitattun Labaran Safiyar Alhamis

Yau 12 ga watan Disamba, 2019 wanda yayi daidai da 15 ga watan Rabiu Thani Hijira ta 1441.

Ga Cikakkun Labaran:

Sanatoci sun bukaci adinga biyan masu zaman kashe wando albashi tunda gwamnati ta gaza samar da ayyukan yi.

Gwamnatin jihar Kano za ta kafa dokar hana aurar da ‘yan mata kafin su kammala sakandare.

Sanata Shehu ya ce yanan a siyasance Kuma zai kara fitowa takara a 2023.

Fatima Abdullahi, ‘yar uwar Maina uwa daya, uba daya ta nesanta kanta da shi a yayin ba da shaida a gaban kotu.

Gwamnatin jihar Jigawa za ta kashe Naira miliyan 60 wajen gina dakunan ‘ba haya’.

Femi Fani Kayode ya gargadi shugaba Buhari kan yin katsalandan kan shari’ar zaben gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde.

Jami’an tsaro na FBI a Amurka sun kama jirgin wani attajirin dan Najeriya kan zarginsa da damfara da safarar miyagun kwayoyi.

Majalisar Dinkin Duniya ta aike da tireloli 32 dauke da kayan taimako zuwa yankin Idlib na arewacin Siriya.

A wani gidan gona dake yankin Suffolk na Ingila an bayyana bullar murar tsuntsaye.

Dada bangaren wasanni kuwa zakuji cewar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta bayyana cewar har yanzu hukumar kwallon kafa ta kasar nan bata biyasu kudinsu ba na gasar Aiteo Cup da suka lashe wato naira miliyan 25.

Ajiya aka kammala wasannin rukuni na gasar cin kofin zakarun nahiyar turai.

Ayau za a fafata wasannin gasar ajin kwararru ta nahiyar turai.

Check Also

Right Honourable Cidari 1

KNHA pledged to support Community Promotion Council…. Speaker Chidari.

Kano State House of Assembly has reiterated its support to Kano Promotion Council on its …