Tattaunawa da Matashi Mai Dalilin Aure dan Shekaru 23

AR_ Gabatar mana da kanka da kuma aikace aikace da kake yi.
Auwal_ sunana Auwal Faruq Idris, ina da wata gidauniya ta hada aure tsakanin samari da yammata da zawarawa , a wannan gidauniyar tawa ba karbar kudi muke ba kurum muna yi ne bias bilillahi.

AR_ shekarun ka nawa yanzu kuma shekarun ka nawa ka na wannan aiki?
Auwal_ shekara ta 23, kuma yanzu shekaruna biyu ina wannan aikin

AR_ Ya kake ji idan ana kiranka da mai dalilin aure, kana jin bacin rai idan ankiraka da hakan?
Auwal_ ina mutukar jin dadi kuma bantaba jin bacin rai ba, karewa ni dadi nake ji domin sunnar annabi nake hadawa ba shakiyanci ba.

AR_ kai kana da aure?
Auwal_ ina dab da yi dai

AR_ Tunda kana tare da mahaifanka kake wannan aiki sun taba kokarin hana ka?
Auwal_ a’a kullum kara karfafamin gwiwa sukeyi domin cigaba da wannan aikin.

AR_ Aure nawa ka hada zuwa yanzu?
Auwal_ gaskiya suna da yawa

AR_ A yanzu a kasa kana da wasu wadanda suka kawo nasu suna neman miji?
Auwal_ akwai kusan goma sha, wadanda suka bayar kuma idan akwai namijin da yake so zai iya zuwa.

AR_ Shin ya maganar gwaji kafin aure?
Auwal_ ai kafin ayi aure sai mun tabbata anyi gwaji.

AR_Ya kake aiwatar da bincike don tabbatar wanda ya zo neman mata koi ta wacce ta kawo nata nemna mijin aure?
Auwal_ ai sai munyi bincike akan mutum, ko da kuwa ya kawo mana hotonsa don sai ya cike fom wanda ta nan zamu bi muyi bincike akansa, haka su ma mata kowacce takan cike fom kafin mu karbi hoton ta.

AR_ Menene burinka a wannan aikin da kake?
Auwal_ burina shine watarana wannan cibiya tawa ta shiga wasu jahohin.

Check Also

Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin kisan da Babbar Kotun ta yanke a kan Maryam Sanda

Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin kisa da Babbar Kotun Birnin …

error: Alert: Is not allowed !!!