Wani Dan Majalisa a Najeriya na Shirin Sayen Kungiyar Kwallon Kafa ta Arsenal

Dan majalisa mai wakiltar Abia a Majalisa Orji Uzor Kalu ya na son zuba jari a Arsenal. Tsohon Gwamnan jihar Abia ya ce zai saye 35% na hannun jarin kungiyar.

Kalu ya bi sahun Aliko Dangote da ya ke da burin fansar kungiyar kwallonOrji Uzor Kalu, Sanatan da ke wakiltar arewacin jihar Abia a majalisar dattawa ya kudiri niyyar sayen kashi 35% na hannun jarin kungiyar Arsenal.

Sanata Orji Uzor Kalu ya yi gwamna tsakanin 1999 zuwa 2007, ya ce yanzu burinsa shi ne ya zuba jari a kungiyar ta yadda za ta kai ga samun nasarori.A tarihi, kungiyar kwallon kafan Arsenal ba ta taba samun nasarar cin gasar ‘Champions League’ ba, Kalu ya na sa rai zai kai kungiyar ga wannan nasara.

Uzor Kalu ya bayyana cewa ya na da burin ganin Arsenal ta lashe gasar Firimiya sau biyu a jere. Abin da kungiyar Ingilar ta shafe shekaru ba ta yi ba. A lokacin da ya ke gwamna a Abia, kungiyar kwallon Enyimba da ke garin Aba ta lashe gasar Firimiyan Najeriya a 2001, 2002, 2003, 2005 da 2007.

“Nasarar da mu ka samu da kungiyar kwallon kafan Enyima tsakanin 2000 da 2007, ya kara mani sha’awar wasan kwallon kafa.” Inji Orji Uzor Kalu.

Sanatan ya ce a Facebook: “A matsayina na jigon wasanni a Afrika, ina tunanin zuba kudi a harkar kwallo, don haka zan saye 35% na kungiyar Arsenal.”
“Burinmu shi ne mu dauki kofin Champions League da Firimiya sau biyu a jere, kamar yadda mu ka yi da Enyimba.”Kafin ‘dan siyasar, tun ba yau ba, mai kudin Najeriya da nahiyar Afrika, Aliko Dangote ya shaida wa Duniya cewa zai nemi sayen kungiyar Arsenal.

Check Also

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo mai shekara …

error: Alert: Is not allowed !!!