Wata kotun a birnin Beijing ta kasar China ta umarci wani mutum ya biya matarsa fansar kudaden aikace aikacen gidan da ta yi masa kafin ya sake ta.

Wata kotun a birnin Beijing ta kasar China ta umarci wani mutum ya biya matarsa fansar kudaden aikace aikacen gidan da ta yi masa kafin ya sake ta.

Zai biya matar kudin da suka kai yuan 50,000 kwatankwacin dalar Amurka 5,460 na tsawon bautar da ita da ya yi shekara 5.

Wannan shari’a ta janyo cece kuce a kafafen sada zumunta akan kimar aikace aikacen gida, inda wasu ke cewa kudin da zai biya sun yi matukar yin kadan.

Wannan hukunci dai na zuwa ne bayan China ta gabatar da wani sabon kundin doka da zai shafi fararen hula.

Daga bayanan kotun, mutumin ne ya nemi rabuwa da matarsa wadda ya aura a shekarar 2015.

Da farko dai ta amince a rabu, amma daga baya ta nemi a biya ta wasu kudade, saboda mijin nata baya aikin komai a gidan ba kuma ya kula da yaransu.

Check Also

Gwamantin Tarayya ta ce ba za ta tattauna da ’yan bindiga da ke addabar sassan kasar nan. Yayin jawabi ga Taron Tattaunawa kan Taron Kasa a Fadar Shugaban Kasa, Mashawarcin Shugaban Kasa kan Tsaro, Janar Babagana Monguno (mai ritayi) ya yi fatali ta batun sulhu da ’yan bindiga. Fitaccen malamin Islama, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, wanda kuma tsohon hafsan soja ne na daga cikin masu ba da shawarar tattaunawar sulhu da ’yan bindigar domin a samu zama lafiya. Amma da yake bayani a Fadar Shugaban Kasa a jiya Laraba, Monguno ya ce yin sulhu zai sa ’yan bindigar su yi zaton cewa gwamanti ta gaza. Ya ce, “Gwamnati na kokarin shawo kan matsalar tsaro, kuma sun sha bayyana cewa akwai matakai biyu na magance ta –lallami, tattaunawa, da sauransu. Duk da cewa gwamnati ba ta adawa da tattaunawa da su, amma tsakanin da Allah dole gwamnati ta yi amfani da karfi a kan wadannan mutane saboda ba su da amana, tunda za’a yi magana da su amma su je su wani na daban kuma su ci gaba da cutar da al’umma

Gwamnatin Tarayya tace babu shulhu tsakanin ta da ’yan bindiga da ke addabar sassan kasar nan

Gwamantin Tarayya ta ce ba za ta tattauna da ’yan bindiga da ke addabar sassan …

error: Alert: Is not allowed !!!