Yadda Akayi Bikin Buɗe Gasar Firimiya ta Mata ta Najeriya

Ayammacin jiya Laraba 9 ga watan Disamba akayi bikin buɗe sabuwar kakar wasa ta mata ta Firimiyar Najeriya wato kakar wasa ta 2020 zuwa 2021 kenan.

Anyi bikin buɗe gasar ne a Lafia babban birnin Jahar Nasarawa kuma karon farko ansami ministoci guda biyu sun halacci wannan bikin buɗe gasar wato Sunday Dare da kuma Paulen Tallen inda dukkaninsu sunje jahar ta Nasarawa.

Anyi bikin buɗe gasar ne tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafan mata ta Nasarawa Amazons da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa tal F/C Robo Queens inda Nasarawa Amazons ta kwashi kashinta ahannu daci ɗaya mai ban haushi.

Ga yadda sakamakon sauran wasannin yake a sassa daban-daban na ƙasar nan tsakanin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar matan:

Abia Angels 2 – Pelican Stars.

Confluence Queens 1 – 1 Rivers Angels.

Ibom Angels 0 – 1 Osun Babes.

Delta Queens 4 – 1 DreamStar.

Nasarawa Amazons 0 – 1 FC Robo Queens.

Bayelsa Queens 2 – 1 Sunshine Queens.

Check Also

Ƙungiyoyin Ƙwallon Ƙafan Dasukafi Jefa Ƙwallaye Abana

Akakar wasa ta bana a manyan gasar rukuni-rukuni ta ƙasashen turai guda biyar da ake …

error: Alert: Is not allowed !!!