Yadda Muka Samu Silin Gashin Manzan Allah a Kano-Sheik Qariballah Nasiru Kabara

Shugaban darikar kadiryya na Afrika Sheik Kariballah Sheik Nasir Kabara ya ce Allah ya albarkanci su da samun silin gashin kan Mamzon Allah (S.A.W) a gidan Kadiryya na Kano.

sheik Karibullah ya yi wannan bayanine a hirar da ya yi da gidan rediyon Faransa a nan Kano.

Ya ce sun samu gashin daga wurin wadanda suka gajeshi tun iyaye da kakanni.Malam Kabara ya ce asalin gashin ya fito ne daga wani sahabi da ake cewa sayyadina Rifa’atu, wanda yana daga cikin wadanda manzan Allah ya baiwa gashinsa lokacin da aka yi masa aski.

“Allah ya girmamamu da samun wannan albarka ta wannan abu na jikin manzan (SAW) shi ne gashinsa.
“Kamar yadda yazo a cikin sahihan littafai na musulunci, a cikin sahihul Buhari, Annabi (SAW) lokacin da yayi hajjin bankwana anyi masa aski, an aske gashin kansa baki daya.

“Ya kuma dauki gashinnan ya rarrabawa sahabban sa ya bawa wasu da yawa, wasu guda goma wasu ashirin, wasu akwai wanda ya bashima sili daya.

“To shi gashin Manzan Allah kamar yadda ya ingata yana da wani abin mamaki da yake tattare da shi, shi ne baya balbalcewa, baya lalacewa indai an sameshi to indai shi ne ko shekara nawa zai yi baya lalacewa.

“Wadanda suke da riko da gadon wadannan kaya sunann da abinsu, indan kayi sa’a suna iya sammaka.
“To mu munyi sa’a wanda yazama sun gaji wannan abin a gidan su, ya girmamamu da sili daya na wannan gashin yanzu haka yana tare da mu a nan gidan Kadiriyya.

“Wannan gashi mun sameshi tare da cikakken tarihinsa, ya gada daga mahaifinsa wane, shi ma daga mahaifinsa wane, har zuwa gurin sahabin da manzon Allah ya dankamasa, shi ne sayyadina Rifa’atu Rabiyyallahu anhu.

“Sanadin namu yana nan a rubuce da sa hannu da izini, shima sai da ya nemi izini masu hakki akan abun sanna ya bamu.”a cewar sa.

Malam Kabara ya ci gaba da cewa bayan da aka danka musu gashi sai da aka basu sharadin cewar za su kula da shi fiye da dukiyar su da komai na su.

Check Also

Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin kisan da Babbar Kotun ta yanke a kan Maryam Sanda

Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin kisa da Babbar Kotun Birnin …

error: Alert: Is not allowed !!!