Yan Najeriya ku Zabi 1, Biyan Albashi ko kuma Biyan Tallafin Mai>>Gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa sai dai ‘yan Najeriya sun zabi abi daya tsakanin ci gaba da biyan tallafin man fetur ko kuma biyan Albashi.

Karamin Ministan mai, Timipre Sylva ne ya bayyana haka a fadar shugaban kasa, Muhammadu Buhari bayan ganawa da shugaban kasar.Yace ba’a Najeriya ne kadai ba, Farashin mai yayi kasa, Kudin shiga daga FIRS suma sun yi kasa, samun kudin gwamnati ya ragu da kaso 60 cikin 100.

Yace domin haka dolene a daina Biyan tallafin mai dan gwamnati ba zata iya ba. Yace amma nan gaba ‘yan Najeriya zasu saba da hakan saboda a baya ma an cire na Kalanzir kuma yanzu an saba ballantana mai da yawanci masu hannu da shunine ke amfani dashi.

Yace suna magana da wani yake ce masa mutane saidai su zabi daya, idan aka ce a ci gaba da bayar da tallafin man fetur to ba lallai ba a iya ci gaba da biyan albashi ha.

Check Also

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo

Paris St-Germain na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Juventus da Portugal Cristiano Ronaldo mai shekara …

error: Alert: Is not allowed !!!