Yan Sanda_ DPO Mai Duka da Tabarya a Arewacin Najeriya

Ana zargi wani baturen yan sanda da ke ofishin ‘yan Sanda na Township a jihar Bauchi da azabtar da wasu matasa guda uku, bisa zargin satar kaji guda 7, wanda biyu daga cikin matasan suka mutu, a yayin da dayan kuma ya karye a kafafuwansa.

Binciken ya nuna cewar baturen yansandan suna, SP Baba Muhammed ya yi kaurin suna wajen azabtar da mutane ta hanyar duka da tabarya, kamar yadda abokin yaran biyu da suka mutu, mai suna Abdulwahab Bello, wanda shi kuma yarasa kafafuwansa ya shaidawa wakilin kafar yada labarai ta Muryar Amurka.

Daya daga cikin mahaifiyar da dan nata ya mutu a hannun ‘yan sanda ta ce, ita tana son a bi mata kadin danta da aka kashe.

An gurfanar da kwamishinan ‘yan sandan jihar ta Bauchi, da baturen yansandan din da ake zargi SP Baba Muhammed gaban babban kotun tarayya da ke Bauchi, a cewar lauyan da ya shigar da karar.
Hukumar ‘yan sandan jihar ta yi bayani a hukumance kan batun tabakin kakakinta DSP Muhammed Wakil inda ya ce kwamishinan ‘yan sanda ya kafa kwamitin da zai yi bincike kuma duk dan sandan da aka kama da cin zarafi, hukumar za ta hukuntashi.

A halin da ake ciki dai gwamnatin jihar Bauchi ta kafa kwamitin binciken duk wani lamari na zargin cin zarafin bil adama da jami’an ‘yan sandan SARS ke aikatawa karkashin babban mai sharia, Habibu Idris Shall.

Check Also

Tattaunawa da Matashi Mai Dalilin Aure dan Shekaru 23

AR_ Gabatar mana da kanka da kuma aikace aikace da kake yi. Auwal_ sunana Auwal …

error: Alert: Is not allowed !!!