An sami k’arin mutune 571 da suka kamu da annobar corona virus a kasarnan

Hukumar dakile cututtuka masu yaduwa a kasar nan ta NCDC ta ce an samu karin mutum 571 da suka kamu da annobar cutar Corona a kasar nan jiya Talata.

Kamar yadda aka sani a mafiya yawan lokuta jihar Legas ce ke kan gaba cikin jerin jihohin da ake samun yawaitar bullar cutar, inda a jiya mutum 170 aka tabbatar sun kamu.

Alkaluman hukumar sun nuna cewa an samu mutum 65 a jihar Ogun da gwajin da aka yi musu ya nuna cewa sun kamu, abin da ke nufin cewa jihar ce ta biyu a wannan rana.

Mutum 45 kuma sun kamu da ita a garin Abuja babban birnin tarayya, sai jihar Kwara da aka samu mutum 34 da jihar Abia mai mutum 32 sai jihar Enugu mai mutum 32.

Anan jihar Kano an samu mutum 25, yayin da karin mutum 22 suka kamu a jihar Oyo, jihar Ondo kuma na da mutum 21.

Check Also

IMG Spraker Falgore

KNHA okays Governor Abba Kabir to appoints 25 Special Advisers

KNHA okays Governor Abba Kabir to appoints 25 Special Advisers The State House of Assembly …