Hukumar da ke sanya ido akan ingancin abinci da sauran abubuwan amfani ta jihar nan ta ce, ya zama wajibi a rika yi wa masu gidajen siyar da abinci gwajin lafiya

Hukumar da ke sanya ido akan ingancin abinci da sauran abubuwan amfani ta jihar nan ta ce, ya zama wajibi a rika yi wa masu gidajen siyar da abinci gwajin lafiya game da cutukan da za’a iya yadawa irin su tarin fuka da cuta mai karya garkuwar jiki da kuma  ciwon hanta.

Shugaban hukumar na riko Baffa Babba Dan Agundi ne ya bayyana hakan, yana mai cewa an dauki matakin ne domin tsaftace jihar daga dukkan wasu gurbatattun abinci domin kiyaye lafiyar jama’a.

Dan Agundi ya kara da cewa duk wanda aka gwada aka ga ya kamu da daya daga cikin wadannan cutukan za’a haramta masa sayar da abinci domin kare lafiyar al’umma.

Ya kara da cewa za’a fara gwajin ne cikin wata mai kamawa na Maris, tare da jaddada cewar za’a ringa yin rijistar kyauta, kuma hukumar ba za taji nauyin rufe duk wani waje da ya nemi yayi wasa da doka ba.

Check Also

IMG Spraker Falgore

Capacity building ; a morale booster for effective service delivery.. Speaker Falgore.

From the Legislative House, Kano State House of Assembly. Capacity building ; a morale booster …