Gwamnatin Tarayya ta gargadi ’yan kasar nan cewa bullar cutar Ebola a makwabtakan kasar na barazana gare ta, yayin da aka gano masu dauke da sabon nau’in cutar COVID-19 mai saurin kisa a kasar.
Shugaban Kwamitin yaki da COVID-19 (PTF) kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya ce kasar nan za ta tsaurara matakan tantance lafiya a hanyoyin shiga kasarta musamman daga kasashen Guinea da Congo da aka samu bullar cutar Ebola.
Boss Mustapha ya kara da cewar wannan nauyi ne ba a kan gwamnati kadai ba, daukacin ’yan kasar nan da sauran jama’a ma na da rawar da za su taka.