Sufeto Janar na ‘yan Sanda na kasa ya bayar da umarnin gaggawa domin tabbatar da zaman lafiya a Jihar Oyo

Sufeto Janar na ‘yan Sanda Mohammed Adamu, ya bayar da umarnin gaggawa na tura dakarun tabbatar da zaman lafiya zuwa Jihar Oyo da ke kudu maso yammacin ƙasar.

Umarnin na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sadan kasar nan Frank Mba, ya sanya wa hannu ranar Litinin domin dawo da zaman lafiya a rikicin da aka yi a ranakun Juma’a da Asabar.

Mista Mba ya ce an tura dakarun ne domin dawo da zaman lafiya tare da tabbatar da doka da oda a wuraren da aka yi rikici tsakanin Hausawa da Yarabawa a ƙarshen mako.

Hausawa aƙalla 10 aka kashe da kuma Bayarabe ɗaya yayin rikicin.

Dakarun waɗanda akasari suka ƙunshi masu tattara bayanan sirri da kuma na fagen daga, sun ƙunshi ɓangare huɗu na ‘yan sanda; dakarun kwantar da tarzoma, ƙwararru wurin tattara bayanai, jirgin helikwafta na sashen ‘yan sandan sama, a cewar sanarwar.

Check Also

IMG Spraker Falgore

Capacity building ; a morale booster for effective service delivery.. Speaker Falgore.

From the Legislative House, Kano State House of Assembly. Capacity building ; a morale booster …