Yadda Aka Raba Kyaututtuka Ga ‘Yan Wasan Afrika

 

Ajiya Talata 7 ga watan Janairu na 2020 akayi bikin karrama ‘yan wasan kwallon kafa na nahiyar Afrika bangaren maza da bangaren mata.

Inda akayi bikin karrama’yan wasan akasar Masar wadda itace ta dauki nauyin gasar cin kofin nahiyar Afrika data gabata.

Idan muka fara da bangaren maza dan wasan kasar Senegal wato Sadio Mané shine ya lashe gwarzon dan wasan nahiyar Afrika inda ya doke abokan takarar sa wato Mohammed Salah da Mahrez.

Shikuwa Achraf Hakimi na kasar Morocco shine ya lashe gwarzon na matashin dan wasa na nahiyar Afrika.

Djamel Belmadi na kasar Algeria shine ya lashe kyautar gwarzon mai horas wa.

Haka kasar ta Algeria ita aka zaba amatsayin kasar datafi kowacce kasa iya taka leda a nahiyar ta Afrika.

Haka anzabi kwallon da Riyad Mahrez ya jefawa Najeriya amatsayin kwallon datafi kowacce kyau a nahiyar Afrika.

Idan muka koma bangaren mata kuwa suma ga yadda rabon kyaututtukan ya gabata.

Anzabi ‘yar wasan kasar Najeriya wato Asisat Oshola amatsayin wadda ta lashe kyautar gwarzuwar ‘yar wasan nahiyar Afrika.

Ita kuwa Desiree Elis ta kasar Afrika ta kudu ita aka zaba amatsayin gwarzuwar mai horas wa.

Anzabi tawagar kasar Cameroon ta bangaren mata amatsayin kasar datafi kowacce iya taka leda a nahiyar Afrika.

Haka anfitar da ‘yan wasa mutane 11 dasuka fi iya taka leda a nahiyar Afrika,

Ga jerin’yan wasan kamar haka:

Mai tsaron gida, anzabi Andre Onana na kasar Cameroon.

Masu tsaron baya kuwa sune kamar haka

Achraf Hakimi da Koulibaly da Joel Motip da kuma Serge Aurier.

Sauran ‘yan wasan tsakiya da ‘yan wasan gaba sun hadar da Riyad Mahrez da Idrissa Gana da Hakim Ziyech da Mohammed Salah da Sadio Mané da kuma Aubameyang.

Check Also

IMG 20240425 WA0009

SWAN Kano Executives Visit Salisu Musa Jegus, Express Radio Staff, After Car Accident

By Muzammil Dalha Yola Today tuesday, the executive members of the Sports Writers Association of …