Jam’iyyar Adawa ta PDP ta yi martani kan hukuncin Kotun Koli

Babbar Jam’iyyar hamayya a Najeriya PDP ta ce ta yi mamakin hukuncin da kotun koli ta yanke kan zaben gwamnan jihar Imo

A ranar Talata ne kotun koli ta kwace kujerar gwamna daga Emeka Ihedioha na Jam’iyyar PDP ta baiwa Hope Uzodinma na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.

Sanarwar da kakakin jam’iyyar PDP Kola Ologbondiyan ya fitar bayan zartar da hukuncin ta ce, PDP ta kasa fahimtar dalilan da kotun koli ta yi dogaro da su na yanke hukuncin.

PDP ta kasa fahimtar yadda za a ce dan takarar da ya zo na hudu a zaben gwamna na 9 ga Maris da kuri’a 96,458 ace ya doke dan takarar PDP da ya samu yawan kuri’u 276,404

Sai dai kuma jam’iyyar APC ta bayyana farin cikinta da hukuncin Kotun kolin da ta bayyana dan takararta Hope Uzodinma a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Imo.

Check Also

Fa'izu Alfindiki

Shugaban karamar hukumar Fa’izu Alfindiki zai bada karfi wajan ingata lafiya a karamar hukumar Birni

Shugabancin karamar hukumar birnin Kano yace zai hada kai da daukacin jami’an lafiya wajen inganta …

error: Alert: Is not allowed !!!